Feb 25, 2019 15:08 UTC
  • Iran: An Shiga Rana Ta Uku A Atisayin Sa Sojojin Ruwa Suke Gudanarwa

An shiga rana ta uku a atisayin da rundunar sojin ruwa ta kasar Iran ke gudanarwa a cikin tekun Fasha da tekun Oman har zuwa tekun India.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, ma'ikatar tsaron Iran ta cewa babbar manufar atisayin dai ita ce gwada jiragen ruwa na yaki masu tafiya karkashin ruwa (submarines) da Iran da kera, da kuma yadda za su iya harba manyan makamai masu linzami zuwa doron kasa, da kuma jiragen ruwa na yaki masu tafiya kan ruwa, wadanda za su iya harba makamai zuwa doron kasa da kuma cikin sararin samaniya, kuma dukkanin gwaje-gwajen sun gudana a cikin nasara.

Rundunar sojin ruwa ta kasar Iran ta sanar da cewa, wannan atisayi na a matsayin kara damara ne da kuma zama cikin shirin ko ta kwana, domin tunkarar kowace irin barazana daga makiya, kamar yadda rundunar sojin ruwa ta kasar Iran din ta ce tana sanya ido matuka kan dukkanin abubuwan da suke kai da komowa a cikin tekun fasha da ma yankin gabas ta tsakiya baki daya.

Tags