Feb 23, 2019 06:59 UTC
  • Iran: An Fara Gudanar Da Gagarumin Atisayin Sojojin Ruwa Mai Taken

A jiya rundunar sojin ruwa ta kasar Iran ta fara gudanar da wani gagarumin atisayi na tsawon kwanaki uku mai taken "Wilyah 97".

Mai magana da yawun atisayin Admiral Hamza Ali Kaviyaniya bayyana cewa, atisayin na gudana nea  cikin tekun Fasha da kuma Tekun Oman zuwa tekun India.

Ya ce a wannan atisayi rundunar sojin ruwa ta Iran za ta gwada wasu sabbin jiragen ruwa na yaki "submarine" masu tafiya karkashin teku wadanda kasar ta kera, inda ya ce wadannan jiragen ruwa masu tafiya karkashin kasa a karon farko za su harba makamai masu linzami daga karkashin teku zuwa wuraren da aka saita sua  doron kasa.

Bayan hakan kuma ya ce, za a gwada wasu manyan jiragen ruwa na yaki masu tafiya  akan doron ruwa, wadanda jiragen yaki masu saukar angulu suke sauka a kan tare da daukar mayaka ko sauke makamai, kamar yadda wadannan jirage su ma suke iya harba manyan makamai masu linzami zuwa tazara mai nisa a kan doron kasa.

Admiral Ali Hamza ya ce rundunar sojin ruwa ta Iran tana gudanar da wannan atisayi ne domin kara zama cikin shirin  ko ta kwana, domin fuskantar kowace irin barazana daga makiya.

Tags