Nov 06, 2018 05:25 UTC
  • Dakarun Iran Sun Kaddamar Da Wani Gagarumin Atisayen Kare Kasar Daga Hare-Haren Makiya

Dakarun kasar Iran sun kaddamar da wani gagarumin atisayen soji na shekara-shekara da suke yi don gwada irin karfi da kuma shirin da suke da shi wajen kare sararin samaniyyar kasar daga hare-haren makiya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran (IRNA) ya ce a jiya Litinin ne aka fara atisayen na kwanaki da aka ba shi sunan Atisayen Masu Kare Sararin Samaniyyar Wilaya ta 2018, inda za a gudanar da atisayen na hadin gwiwa tsakanin dakarun sansanin kare sararin samaniyya na Khatam al-Anbiya, dakarun kare sararin samaniyya na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran din da kuma rundunar sojin sama na Iran.

Mukaddashin babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Rear Admiral Habibollah Sayyari wanda kuma shi ne yake jagorantar atisyen ya shaida wa manema labarai cewa atisayen zai hada yankunan da suka kai fadin murabba'in kilomita 500,000 a yankunan arewa, yamma, gabashi da kuma tsakiyar kasar ta Iran, yana mai cewa dukkanin makamai da na'urorin da za a gwada a yayin atisayen, kwararrun kasar Iran ne suka tsara da kuma kera su.

Yayin da yake magana kan takunkumin da Amurka ta sanya wa Iran wanda aka fara atisayen a daidai lokacin da aka sanya shi, Admiral Sayyari yace koda wasa takunkumin ba zai shafi shirin Iran na kare kanta daga barazanar makiya ba.

 

Tags