Iran Zata Gina Gidaje Dubu 200 A Kasar Siriya
Shugaban kungiyar Inginiyoyi a nan Tehran ya ce kasar Iran ta cimma yerjejeniya da gwamnatin kasar Siriya na gida gidaje dubu 200 a kasar ta Siriya
Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Irj Rahbar mataimakin shugaban kungiyar inginiyoyin yana fadar haka a yau a nan birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa mafi yawan gine-ginen za'a yisu ne a birnin Damascus babban birnin kasar ta Siriya.
Rahbar ya kara da cewa mai yuwa a fara aikin gine-ginen nan da watannu uku masu zuwa.
Gwamnatin kasar Iran dai tana tare da kasar Siriya tun shekara ta 2011 a lokacinda yan ta'adda suka mamaye mafi yawan kasar. Kuma ta sha nana cewa zata taimaka wajen ganin an sake gina kasar bayan nasarar da aka samu kan kungiyoyin yann ta'adda a shekarar da ta gabata