-
Jami'an Tsaron Kasar Iran Sun Kama Yan Ta'addan Da Suka Kashe Sojojin Kasar A Garin Sarboz
Aug 26, 2017 08:16Rundunar dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun sami nasara capke yan ta'adda wadanda suka kashe dakarun juyin juya halin musulunci biyu da kuma wani mayakin sa kai wato basij a kan iyakar kasar da kasar Pakistan.
-
Hukumar IAEA Bata Da Hurumin Binciken Rumbunan Ajiye Makaman Kasar Iran
Aug 23, 2017 07:20Komitin tsaro da harkokin kasashen waje na majalisar dokokin JMI ya ce hukumar IAEA bata da hurumin binciken rumbunan ajiye makaman kasar Iran .
-
Sabon Jakadan Najeriya A Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga Ya Gana Da Dr. Zarif
Aug 22, 2017 09:53Sabon jakadan Najeriya a Jamhuriyar Musulunci ta Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga, ya gana da ministan harkokin wajen Iran Dr Muhammad Jawad zarif.
-
Jakadun Mali da Nigeria Sun Gana Da Ministan Harkokin wajen Iran
Aug 22, 2017 02:04Jakadun kasashen Mali, Nigeria, Sirilanka da Kuma Jumhuriyar Check sun gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawada Zarif
-
Zarif Ya Jaddada Aniyar Iran Ta Kare Yarjejeniyar Nukiliya Da Kalubalantar Bakar Siyasar Amurka
Aug 21, 2017 02:13Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce kare yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka cimma tsakaninta da manyan kasashen duniya gami da kalubalantar bakar siyasar Amurka.
-
Kuri'ar Amincewa Da Ministocin Sabuwar Gwamnatin Shugaba Hasan Ruhani
Aug 21, 2017 00:44A jiya Lahadi ne dai majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran ta kawo karshen zaman tantance ministoci 17 da shugaba Hasan Ruhani ya gabatar mata don amincewa, inda majalisar ta amince da ministoci 16 kana guda kuma ya gagara samun amincewar majalisar.
-
Burin Iran Shi Ne Kare Yarjejeniyar Nukiliya Saboda Makiya_ Rohani
Aug 20, 2017 06:44Shugaba Hassan Rohani, na jamhuriya musulinci ta Iran ya bayyana cewa babban burin kasarsa shi ne kare yarjejeniyar nukiliyar , saboda abokan gaban kasar a sahun gaba Amurka.
-
Zarif: Babu Ruwan Musulunci Da Ayyukan Ta'addanci Da Ake Yi Da Sunansa
Aug 19, 2017 12:06Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar babu ruwan Musulunci da ayyukan ta'addancin da ake aikatawa da sunansa.
-
Yakamata Amurka Ta Ji Kunyar Magana Kan Take Hakkin Bil'adama - Ayat. Khatami
Aug 18, 2017 14:22Limamin da ya jagoranci sallar jumma'a a nan Tehran Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta ji kunyar bayyana ra'ayinta dangane da take hakkin bil'adama a sauran kasashen duniya.
-
Dr Ruhani Ya Ce: Kungiyar Ta'addanci Ta Da'ish Babbar Misali Ce Ta Munafuci A Wannan Zamani
Aug 17, 2017 14:29Shugaban kasar Iran ya bayyana kungiyar ta'addanci ta Da'ish da masu goya musu baya a matsayin manyan misalai na tushen munafuci da rusa rayuwar al'umma a wannan zamani.