Hukumar IAEA Bata Da Hurumin Binciken Rumbunan Ajiye Makaman Kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23458-hukumar_iaea_bata_da_hurumin_binciken_rumbunan_ajiye_makaman_kasar_iran
Komitin tsaro da harkokin kasashen waje na majalisar dokokin JMI ya ce hukumar IAEA bata da hurumin binciken rumbunan ajiye makaman kasar Iran .
(last modified 2018-08-22T11:30:35+00:00 )
Aug 23, 2017 11:50 UTC
  • Hukumar IAEA Bata Da Hurumin Binciken Rumbunan Ajiye Makaman Kasar Iran

Komitin tsaro da harkokin kasashen waje na majalisar dokokin JMI ya ce hukumar IAEA bata da hurumin binciken rumbunan ajiye makaman kasar Iran .

Muryar JMI ta nakalto Mohammad Jawad Jamali, memba a komitin tsaro da kuma harkokin wajen na majalisar dokokin JMI yana fadar haka a safiyar yau Laraba ya kuma kara da cewa yerjejeniyar PMD tsakanin Iran da manya manyan kasashen duniya kan shirinta na makamashin nukliya ya amincewa hukumar IAEA binciken cibiyoyin sarrafa makamashin nukliya na kasar Iran ne kasai, yerjejeniyar bata ambaci rumbunan makaman kasar ba.

Jamali yana maida martani ne ga Nikki Haley wani dan majalisar wakilan kasar Amurka, wanda ya bayyana cewa hukumar IAEA tana da hukumin binciken duk wani wurin da take shakka a cikin kasar Iran daga ciki har da rumbunan makaman kasar. Jamali ya kammala da cewa yin haka keta hukumar kasar ne kuma iran ba zata taba amincewa da hakan ba.