Aug 22, 2017 14:23 UTC
  • Sabon Jakadan Najeriya A Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga Ya Gana Da Dr. Zarif

Sabon jakadan Najeriya a Jamhuriyar Musulunci ta Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga, ya gana da ministan harkokin wajen Iran Dr Muhammad Jawad zarif.

A jiya ne 21 ga watan gusta 2017 sabon jakadan tarayyar Najeriya a jamhuriyar muslunci ta Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif.

Dukkanin bangarorin biyu na Iran da Najeriya, sun jaddada wajabci ci gaba da kara bunkasa alaka a tsakaninsu a dukkanin bangarori, musamman harkokin kasuwanci da kuma bunkasa tattalin arziki.

Iran da Najeriya dai suna dadaddiya dangantaka ta diflomasiyya, kuma dukkanin kasashen biyu mambobi ne a kungiyoyi daban-daban, da suka hada da OPEC, da kuma kngiyar kasashe masu fitar da isakar gas , haka nan kuma mambobi ne na kungiyar D8.

Tags