Burin Iran Shi Ne Kare Yarjejeniyar Nukiliya Saboda Makiya_ Rohani
Shugaba Hassan Rohani, na jamhuriya musulinci ta Iran ya bayyana cewa babban burin kasarsa shi ne kare yarjejeniyar nukiliyar , saboda abokan gaban kasar a sahun gaba Amurka.
Dr Rohani ya ce abunda ma'aikatar harkokin wajen kasarsa ta sa a gaba shi ne yin duk abunda ya dace domin kare yarjejeniyar da aka cimma da mayan kasashen duniya a shekara 2015, ta hanyar yin katsin landa ga Amurka na cimma manufofinta na siyasa.
Ruhani dai ya ambato wasu kasashe da suka hada da Amurkar da H.K Israila da kuma wasu kasashen yankin da ya danganta da kanana na rushe yarjejeniyar.
Zababen shugaban kasar ta Iran ya bayyana hakan ne a wani jawabinsa a gaban 'yan majalisar dokokin kasar a yau Lahadi, a yayin zaben tantance jerin sunayen mutanen da ya gabatar ga majalisar don nada su a sabuwar gwamnatinsa.