Pars Today
Iran, ta ce kamfanoninta a shirye suke wajen sake gidan kasar Siriya da yaki ya daidaita.
Kasar Iran ta gudanar da bukukuwa na ranar fasahar Sararin samaniya na kasar.
Mukadashin kwamandan rundinar kare juyin juya halin Musulinci na Iran, (IRGC), Birgediya Janar Salami, ya ja kunnen kasashen turai akan duk wani yunkurinsu na raba Iran da makamanta masu linzami na kare kanta.
Jumhuriyar Musulunci ta Iran ita ce kasa da 22 a duniya wajen kera kayaki masu inganci .
Iran ta sanar da harba wani makami mai linzami cikin nasara a yau Asabar, a daidai lokacin da kasar ta fara bukukuwan zagayowar ranakun cika shekaru arba'in cif da nasara yuyin juya halin musulinci na kasar.
Kwararru a ma'aikatar tsaron kasar Iran sun sami nasara kera wani sabon makamai mai linzami mai cin dogon zango.
Limamin da ya jagoranci sallar Jumma;a a nan tehran Aya. Imammi Khashani ya bukaci mutanen kasar Iran su fito konsu da kwarkotansu a ranar 22 ga watan Bahman na wannan shekara don nuna goyon bayansu ga juyin juya halin musulunci a nan Iran.
Bayan an dade ana jira, daga karshe kasashen Turai sun kaddamar da kafar sadarwa ta kasuwanci tsakaninsu da JMI a yau Alhamis.
A yayin da kungiyar tarayyar turai ke da'awar cewa nan ba da jimawa ba za ta samar da wata hanyar saukaka mu'amalar kasuwanci da kasar Iran, hukumomin birnin Tehran sun gargadi kungiyar da rashin cika alkawari.
Jakadan kasar Iran a Iraqi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran a shirye take ta taimaka wajen sake gina kasar Iraqi da kuma tallafawa yan gudun hijirar kasar.