Iran Ta Gudanar Da Bukukuwan Fasahar Sararin Samayiya.
(last modified Mon, 04 Feb 2019 12:02:44 GMT )
Feb 04, 2019 12:02 UTC
  • Iran Ta Gudanar Da Bukukuwan Fasahar Sararin Samayiya.

Kasar Iran ta gudanar da bukukuwa na ranar fasahar Sararin samaniya na kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan tehran ta nakalti ministan yada labarai da kuma fasahar sadarwa Mohammad Jawad Azari yana fadar cewa shirin sarafin samaniya na kasar Iran bai da dangantaka da shirin makamai masu linzami na kasar. Ya kuma kara da cewa akwai manya-manyan kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka gudanar da bicnike a kan shirin, inda suka tabbatar da cewa bai da hatsari ga kowa.

Azari ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta sanyawa shirin fasahar sararin samaniya ta kasar takunkumi amma kuma a wajenmu wata dama ce, don hakan ya sanya muka samar da fasahar da ake bukata don ci gaba da shirin a cikin gida. 

Ministan ya ce kasashen Turai ma basa bada hadin kan da Iran taek bukata a wannan fagen, saboda tauraron dan adama na farko da kasar ta kare tare da taimakon wasu kasashen Turai mai suna "Mesbah" sai da yau dau shekaru 10 turawan suka ki cillashi zuwa sararkin samaniya a cibiyar Gavazzi ta sararin samaniya ta ke kasashen na Turai.

Ya ce a shekara ta 2009 ne Iran ta cillam tauraron dan adam na farko 100/100 fasahar cikin gida zawa sararin samaniya, mai suna Omid. Sai kuma a cekin watan Febrerun shekara ta 2015 ta cilla tauraron dan adam mai suna Fajr zuwa sararin samaniya. 

A watan da ya gabata ne Iran ta cilla wani tauraron mai suna Payom mai tazarar kilomita 500 daga doron kasar, amma misile da ya kaishi sama bai isa inda ake bukata ba, amma kuma ya yi aikin da ake bukata na daukar Hotuna daga wurare daban-daban.