Kamfanonin Iran Na Shirye Wajen Sake Gina Siriya_Zarif
(last modified Tue, 05 Feb 2019 15:28:42 GMT )
Feb 05, 2019 15:28 UTC
  • Kamfanonin Iran Na Shirye Wajen Sake Gina Siriya_Zarif

Iran, ta ce kamfanoninta a shirye suke wajen sake gidan kasar Siriya da yaki ya daidaita.

Ministan harkokin wajen kasar ne Muhammad Jawada Zarif, ya bayyana hakan, a yayin wata ganawa da takwaransa na Siriyar, Walid Mouallem, a birnin Tehran.

Bangarorin biyu sun tattauna kan alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma halin da kasar ta Siriya mai fama da yaki tun cikin shekara 2011 ke ciki.

Mista Zarif, ya bayyana wa takwaransa cewa, kamfanonin Iran a shirye suke wajen yin huldar kasuwanci da Siriya a lokacin sake gina kasar.

Idan ana tune a karshen watan Janairu da ya gabata kasashen Iran da Siriya sun cimma yarjejeniyoyi 11 ciki harda na kasuwanci mai daurewa.

Shugaba Bashar Al'Assad na Siriya ya sha alwashin sake gina kasar ta Siriya, wanda kuma a cewarsa kamfanonin kasashen Iran da Rasha nada mihimiyar rawar da zasu taka a wannan aikin.