-
Iran : Matakin Hana Baki Shiga Amurka, ''Abun Kunya Ne''
Jun 30, 2017 05:12Ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif ya bayyana matakin shugaba Donal Trump kan hana baki daga kasashe shida galibi na musulmi shiga Amurka, da abun ''kunya''.
-
Ministan Harkokin Iran Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Nahiyar Turai
Jun 29, 2017 13:06Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a yau a wasu daga cikin kasashen nahiyar turai, inda ya fara yada zangonsa na farko a birnin Paris na kasar Faransa, daga nan kuma zai isa zuwa kasashen Jamus da Italiya.
-
Iran : Zarif, Zai Kai Ziyarar Aiki A Paris
Jun 29, 2017 04:02A wani lokaci, nan gaba ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, zai isa birnin Paris na Faransa a ci gaba da ran gadinsa a nahiyar Turai.
-
Baki Kimani 400 Zasu Halarci Taron Gidajen Television Da Radio Na Musulunci A Mashad
Jun 29, 2017 01:49Sakataren gudanar da taron gidajen Radio Da Television na Musulunci karo na 9 ya ce akalla baki daga kasashe daban daban 400 ne zasu halarcin taron na bana a birnin Mashad arewa maso gabacin kasar ta Iran
-
Iran: Amurka Tana Wasa Da Wuta A Kasar Syria
Jun 28, 2017 14:29Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce; Halayyar da Amurka ta ke nunawa a kasar Syria da babu tunani a ciki, shi ne wasa da wuta.
-
Zarif: Cinikin Makamai A Gabas Ta Tsakiya Ba Zai Kawo Tsaro A Yankin Ba
Jun 27, 2017 00:49Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad jawad zarif ya bayyana cewa, mayar da yankin gabas ta tsakiya wata kasuwar sayar da makamai, ba zai haifar ma yankin da mai ido ba.
-
Jagora:Yaki Da 'Yan Sahyuniya Wajibi Ne Ga Dukkanin Musulmi
Jun 26, 2017 14:38Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Aliyul Khamenei ya bayyana cewa bisa shara'ar Addinin musulinci, domin kalubalantar mamaye maƙiya ga kasar musulmi, wajibi ne ga ko wani musulimi ya yi gwagwarmaya domin haka yaki da Haramtacciyar kasar Isra'ila ya zama wajibi ga ko wani musulmi.
-
Jagoran Juyin Musulunci Ya Jagoranci Sallar Idi A Birnin Tehran
Jun 26, 2017 00:48Ayatullah Sayyid Ali Khmanei ya kira yi al'ummar musulmi da su ci gaba da riko da ibadu kamar yadda su ka yi a cikin watan Ramadan mai alfarma.
-
Cinikin Da Kasar Ghana Ta ke yi Wa Iran Ya Kusa Rubanyawa Uku
Jun 25, 2017 23:59Iran ta bayyana cewa a shekarar da ta gabata kayan da kasar Ghana take saya Iran sun karu da kaso 170%.
-
Jami'an Tsaro A Iran Sun Kama Yan Ta'adda Kimani 50 A Lardin Kirmansha
Jun 25, 2017 12:58Majiyar jami'an tsaro a kasar Iran ta bayyana cewa tun bayan harin ta'addancin da yan kungiyar Daesh suka kai a majalisar dokoki da kuma haramin Imam Khomaini a nan tehran, sun tsare yayan kungiyar ta Daesh kimani 50 a lardin Kirman sha kadai.