Ministan Harkokin Iran Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Nahiyar Turai
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i21766-ministan_harkokin_iran_ya_fara_gudanar_da_ziyarar_aiki_a_nahiyar_turai
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a yau a wasu daga cikin kasashen nahiyar turai, inda ya fara yada zangonsa na farko a birnin Paris na kasar Faransa, daga nan kuma zai isa zuwa kasashen Jamus da Italiya.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jun 29, 2017 13:06 UTC
  • Ministan Harkokin Iran Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Nahiyar Turai

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a yau a wasu daga cikin kasashen nahiyar turai, inda ya fara yada zangonsa na farko a birnin Paris na kasar Faransa, daga nan kuma zai isa zuwa kasashen Jamus da Italiya.

Bayan isarsa birnin Paris a yau, Zarif ya bayyana cewa akwai alaka tsakanin Iran da Faransa a bangarori na kasuwanci da tattalin arziki, wanda kuma bayan zaben Emmanuel Macron, wannan alaka ta kara bunkasa.

Zarif ya kara da cewa, tun bayan cimma yarjejeniya a kan shirin Iran na nukiliya, an samu ci gaba ta fuskar alaka a bangarori daban-daban a tsakanin Iran da kuma kasashen kungiyar tarayyar turai.

A nasa bangaren kakain ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Kasimi ya fadi yau cewa, Iran za ta iya yin mu'amala ta fuskoki da dama musaman a bangaren kasuwanci da bunkasa ayyukan kamfanoni tsakaninta da kasashe masu 'yancin siyasa daga cikin kasashen nahiyar turai.