Iran : Zarif, Zai Kai Ziyarar Aiki A Paris
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i21752-iran_zarif_zai_kai_ziyarar_aiki_a_paris
A wani lokaci, nan gaba ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, zai isa birnin Paris na Faransa a ci gaba da ran gadinsa a nahiyar Turai.
(last modified 2018-08-22T11:30:19+00:00 )
Jun 29, 2017 08:32 UTC
  • Iran : Zarif, Zai Kai Ziyarar Aiki A Paris

A wani lokaci, nan gaba ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, zai isa birnin Paris na Faransa a ci gaba da ran gadinsa a nahiyar Turai.

Mista Zarif dai zai gana da mahukuntan kasar ta faransa inda zasu tattauna kan mahimman batutuwa da suka hada da alakar dake tsakanin kasashen biyu, sai kuma batun gabas ta tsakiya dama na kasa da kasa.

Faransa dai za ta kasance kasa ta uku da Mista Zarif zai ziyarta a ci gaba da ran gadin da ya soma tun a ranar 26 ga watan nan a nahiyar turai.

Dama kafin hakan ya ziyarci kasashen Jamus da kuma Italiya, kuma dukkan bangarorin sun tattauna kan batutuwa da suka shafi alaka da kuma yaki da ta'addanci.