Pars Today
Wata kotun HKI ta daure tsohon ministan makamashi na haramtacciyar kasar Gonen Segev shekaru 11 a gidan kaso bayan ya amince da cewa ya yi aikin leken asiri wa kasar Iran.
Jami’an tsaron Isra’ila sun kame Falastinawa a yankuna daban-daban da ke kusa da birnin Quds a yau.
Shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya kirayi dukkanin Falastinawa da su a birnin Quds daga zuwa ranar Juma’a.
Rahotanni daga Siriya na cewa mutane 20 ne suka ras arayukansu a wani harin bam da aka kai da mota a gabashin kasar.
Cikin wani sabon ta'addanci, jiragen yakin kawancen saudiya sun kai hari a jihar Hajjah dake arewa maso gabashin kasar yemen tare da kashe fararen hula 6.
Kakakin sojan kasar Yemen, Yahya Sari'i ne ya bayyana haka wata hira da kamfanin dillancin labaru na "Saba'
Wani dan majalisar dokokin kasar ta Iraki, Muhammad al-Baldawi ne ya yi gargadin cewa; Amurka tana kokarin sakin fursunonin 'yan ta'adda a cikin Iraki domin sake ba su damar farfadowa
Minista mai bada shawara kan lamuran harkokin wajen kasar Saudia Adil Al-Jubair ya zargi kasar Iran da goyon bayan yan ta'adda a wani ziyarar da kai kasar Pakistan.
Shugaban kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasar Katar ne ya bayyana cewa; Saudiyyar tana amfani da aikin haji a matsayin wani makamin siyasa
Majalisar dokokin kasar Iraqi ta fara shirye-shiryen ficewar sojojin Amurka daga kasar.