Harin Bam (IS), Ya Yi Ajalin Mutum 20 A Siriya
Rahotanni daga Siriya na cewa mutane 20 ne suka ras arayukansu a wani harin bam da aka kai da mota a gabashin kasar.
Majiyoyi daga yankin sun ce harin na jiya Alhamis, an kai shi ne a kauyen Cheheil a kusa da wani sansanin kawacen mayakan Larabwa da kurdawa dake kokarin fitar da fararen hula da suka makalla a yankin na karshe dake hannun kungiyar (IS).
Daga cikin wadanda harin ya rusa dasu akwai ma'aikata 14 na cibiyoyin wani kamfani man fatur na Al-Omar, da kuma mayakan larabawa da Kurdawa guda shida, a cewar kungiyar kare hakkin bil adama ta OSDH.
Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta (IS), ta dauki alhakin kai harin ta hanyar manhajarta ta Telegram.
Tun a farkon watan Disamba da ya gabata, kimanin mutane 40,000 galibi iyalen mayakan dake ikirari da sunan jihadi ne suka tsere daga yankin a cewar kungiyar OSDH.