Pars Today
Mahukuntan Moscow da Landon sun dawo da huldar diflomatsiya tattaunawa a tsakaninsu bayan shafe watanni 11, tun bayan kiki-kakar da ya shiga tsakaninsu kan batun jami'an leken asirin nan na Rasha Skripal.
A Faransa dubban masu zanga zanga wadanda ake kira masu ''dorawa riga'' ne suka sake fitowa yau Asabar a fadin kasar domin ci gaba da zanga zangar la'antar matakan gwamnatin Shugaba Emanuel Macron kan haraji da kuma tsadar rayuwa.
Wai mutum ya bude wutar bindiga a kan mutane a kusa da birnin Chicago na kasar Amurka, inda ya kashe mutane 5 har lahira.
Wata kotu a kasar Austria Ta soke matakinn da ofishin kula da harkokinn addini a kasar ta dauka na rufe masallatai guda 6 a kasar.
Hukumomi a Indiya, sun yi allawadai da mummunan harin da ya yi ajalin jami'an tsaron kasar akalla 40 a yankin Kashmir.
Shugaban kasar Haiti, Jovenel Moïse, ya yi bayyani, a karon farko bayan shafe mako guda na mummunar zanga zangar da wasu 'yan kasar ke yi, na neman ya yi murabus.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Cuba ta bada sanarwan cewa wasu rundunar sojojin Amurka suna shirin kaiwa kasar Venezuela hare-hare daga wasu tsibaran Carabian.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun fitar da rahotanni kan irin cin zalun da gwamnatin kasar China take yi kan musulmin kasar.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, idan Amurka ta yi gigin kaddamar da harin soji kan kasar Venezuela, to kuwa za ta fuskanci Vietnam ta biyu.
Kasashen uku sun bayyana taron da kasar Amurka ta shiyra da cewa yana da illa