Shugaban Haiti, Ya Yi Raddi Ga Masu Bore
Shugaban kasar Haiti, Jovenel Moïse, ya yi bayyani, a karon farko bayan shafe mako guda na mummunar zanga zangar da wasu 'yan kasar ke yi, na neman ya yi murabus.
A cikin wani jawabinsa a gidan talabijin din kasar, bayan artabun da ya faru tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zangar a birnin Port-au-Prince, Shugaba Moïse, ya bayyana cewa, ba zai yarde kasar ta fada hannun 'yan daba masu dauke da makamai da kumam masu safara muggan kwayoyi ba.
Jawabin da Mista Moïse, na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka, ta sanar da janye jami'an diflomatsiyanta wadanda aikinsu ba zan na wajibi ba, da kuma iyalensu dake da zama a kasar ta Haiti.
Sanarwar da gwamnatin Amurkar ta fitar ta kuma bukaci 'yan kasarta dasu guji zuwa kasar ta Haiti.
Tun dai soma zanga zangar ta Haiti, a ranar 7 ga watan Fabarirun nan, mutum bakwai ne aka rawaito sun rasa rayukansu.
Shugaba Jovenel Moïse, wanda ke shugabancin kasar ta Haiti, yau da shekara biyu, ya yi watsi da duk kiraye kirayen neman ya yi murabus, da kuma neman kafa wata gwamnatin wucin gadi.
Rikicin Haiti, dai ya yi kamari ne bayan fitar da wani bayyani na zargin baba-kere da wasu tallafin kudade na Biliyan Biyar da Venezuela ta baiwa kasar a shekara 2008, wanda kuma ake zargin wasu jami'an gwamnatin kasar da hannu a ciki.