An Shiga Wata Uku Na Bore A Faransa
(last modified Sat, 16 Feb 2019 16:55:58 GMT )
Feb 16, 2019 16:55 UTC
  • An Shiga Wata Uku Na Bore A Faransa

A Faransa dubban masu zanga zanga wadanda ake kira masu ''dorawa riga'' ne suka sake fitowa yau Asabar a fadin kasar domin ci gaba da zanga zangar la'antar matakan gwamnatin Shugaba Emanuel Macron kan haraji da kuma tsadar rayuwa.

Rahotanni daga kasar sun ce dubban mutane ne suka shiga zanga zangar ta yau a Paris babban birnin kasar da kuma sauren biranen kasar a ci gaba da boren da suka fara tun ranar 17 ga watan Nowamba na bara.

Alkaluman da ma'aikatar ciokin gidan kasar ta fitar, sun nuna cewa mutane 10, 200 ne suka shiga zanga zangar ta yau, wadanda suka hada da 3,000 a birnin Paris, wanda ya nuna cewa ana fuskantar ragowar masu shiga boren.

Saidai masu shirya zanga zangar na masu musanta alkalumman da hukumomin kasar ke fitarwa.

Wani daga cikin masu zanga zangar mai suna Jérôme Rodrigues, wanda ya rasa idonsa sakamakon amfani da karfi da jami'an 'yan sanda ke yi kan masu boren, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa, sun kai su 15,000 da fito zanga zangar ta yau, wanda kuma yana nuna yadda adadin masu boren ke rubanyawa.

Zanga zanar da 'yan Faransar ke yi ta dai samo asali kan matakin gwamnati na kara kudaden haraji kan man fetur, zanga zangar da kuma ta bazu zuwa sassan kasar, inda harma ta kai ga kiran murabus din shugaban kasar, lamarin da ya cilastawa gwamnatin ta Macron kiran babban taron muhawara, saidai bisa ga dukkan alamu kiran nasa bai samu karbuwa ba, duba da yadda aka shiga watanni uku na boren, nuna adawa da manufofinsa.