Pars Today
A Faransa, babbar kungiyar kwadago ta kasar CGT, ta fara wani yajin aiki na sa'o'i 24 a dun fadin kasar, don neman karin albashi da kuma wasu kudaden alawus alawus.
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya zargi kungiyar tarraya Turai ta (EU), da kokarin kifar da gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro na kasar Venezuela.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, Majalisar ba za ta shiga wata kungiyar kasashen duniya ba da ke kokarin sasanta rikicin kasar Venezuela.
Ma'aikatar tsaron Amurka ( Pentagon) ce ta sanar da aniyarta ta barin wasu sojoji a cikin kasar Iraki
Babban Kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa daga farkon shekarar 2018 din da ta gabata zuwa yanzu an kwashe bakin haure sama da dubu hudu daga kasar Libiya.
Kakakin shugaban kasar Rasha ya ce kokarin da kasashen Yamma ke yi na amincewa da Juan Guaido madugun 'yan adawan kasar Venezula a matsayin shugaban kasa, katsa landan ne ga al'amuran cikin gidan kasar
Paparoma Francis shugaban Cocin Catholica ya isa birnin Abudabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ko UAE a yau Litinin inda ya gana da yerime mai jiran gado na kasar Mohammad bin Zayed Al-Nahyan.
Shugaba Nicolas Maduro, na Venezuela, ya yi watsi da wa'adin da wasu kasashen turai suka dibar masa na ya shirya sabon zaben shugaban kasa.
Firai Ministan kasar Britania Thereser May ta bada sanarwan cewa kasar zata fice daga tarayyar Turai tare da yerjejeniyar da ta fara cimma da ita.
Rundunar yansanda na kasar Faransa ta bada sanarwan cewa jami'an yansanda 4 ne suka ji rauni a fafatawa da masu zanga-zangar kin jinin tsarin jari hujja a kasar.