MDD:Mun Kwashe Bakin Haure Dubu 4 A Libiya
Babban Kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa daga farkon shekarar 2018 din da ta gabata zuwa yanzu an kwashe bakin haure sama da dubu hudu daga kasar Libiya.
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya habarta hukumar dake kula da 'yan gudun hijra da aikinta ya kasance samar da alaka a tsakanin kungiyoyin kasa da kasa domin karewa da kuma magance matsalolin 'yan gudun hijra da bakin haure a Duniya ta sanar a yau cewa cikin shekarar da ta gabata, ta samu nasarar kwashe bakin haure da suka shiga kasar Libiya da nufin zuwa kasashen Turai sama da dubu hudu, sannan kuma ta yiwa wasu dubu 34 da 505 magani.
Rahoton ya ce har ila kwamitin ya taimakawa iyalai dubu 6 da 219 da kudade, sannan kuma ta raba abinci ga bakin hauren dubu daya da 311.
Babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na Majalisar Dinkin Duniyar ya kara da cewa kimanin mutum dubu 56 da 643 daga cikin bakin hauren dake kasar Libiya suka rubuta sunayensu na neman mafuka a kasashen Turai.
Tun bayan kifar da Gwamnatin marigayyi kanal Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011, kasar ta Libiya ta zama hanyar da bakin haure ke bi domin zuwa kasashen Turai, a halin da ake ciki dai, kasashen na Turai na daukan tsauraren matakai na magance kwararan bakin haure cikin kasashen na su.