Ana Yajin Aikin Gama Gari A Faransa
Feb 05, 2019 16:58 UTC
A Faransa, babbar kungiyar kwadago ta kasar CGT, ta fara wani yajin aiki na sa'o'i 24 a dun fadin kasar, don neman karin albashi da kuma wasu kudaden alawus alawus.
Ko baya ga hakan an gudanar da zanga zanga a fadin kasar yau Talata a yunkurin cilasta wa gwamnatin kasar biyan bukatunsu.
An kiyasta samun zanga zanga a wurare sama da 160, da kuma yajin aiki wanda ya shafi ma'aikatun gwamnati.
A baya bayan nan dai gwamnatin Emanuel Macron, na ci gaba da sha suka kan gazawarta wajen biyan bukatun al'umma musamman masu karamin hali, inda aka kwashe kusan makwanni 12 ana bore a fadin kasar.
Tags