Amurka Za Ta Bar Sojojinta A Cikin Kasar Iraki
Ma'aikatar tsaron Amurka ( Pentagon) ce ta sanar da aniyarta ta barin wasu sojoji a cikin kasar Iraki
A wani rahoton da ma'aikatar harkokin tsaron ta Amurka ta aikewa Majalisar dokokin kasar ta ce; Sojojin kasar za su dade a Iraki saboda ci gaba da yaki da ta'addanci
Wani sashe na rahoton ya kuma ce; Bisa la'akari da yadda kungiyar Da'esh ta kara karfi a Iraki; Bai kamata sojojin Amurka su fice daga Irakin ba.
Ma'aikatar harkokin tsaron na Amurka ta bayyana hakan ne a lokacin da al'ummar Iraki da manyan jami'an kasar suke daukar cewa; Cigaba da zaman sojojin Amurkan ne yake karfafa kungiyar ta Da'esh.
Amurka ta aike da sojojinta ne zuwa Iraki a karkashin abin da take kira rundunar kawance ta kasa da kasa domin fada daa ta'addanci.
Tun dai jami'an Kasar Iraki suka fara neman karin bayani daga Amurkan akan cigaba da girke sojojinta a cikin kasarsu.