-
Majalisar Dattijan Amurka Ta Amince Da Kakaba Takunkumi A Kan Rasha
Jul 27, 2017 23:39Majalisar dattijan kasar Amurka ta amince da kakaba sabbin takunkumai a kan Rasha, bisa zargin cewa Rasha ta yi kutse a cikin harkokin zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Amurka a cikin shekarar da ta gabata.
-
Venezuella : 'Yan Adawa Zasu Fito Zanga-zanga Duk Da Haramcin Gwamnati
Jul 27, 2017 23:32'Yan adawa a Venezuela sun ce zasu fito zanga-zanga gama gari a ranakun Juma'a zuwa Lahadi ranar da za'a gudanar da zaben wakilan majalisar dokokin kasar da shugaban Nicolas Maduro ya bukata.
-
Gwamnatin Rasha Ta Yi Barazanar Korar Jami'an Jakadancin Amurka Daga Kasarta
Jul 27, 2017 14:25Wani jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Idan har shugaban kasar Amurka ya rattaba hannu kan sabon takunkumin da Amurka ta kakaba kan kasar Rasha, to babu shakka Rasha zata maida martani.
-
MDD Zata Gudanar Da Bincike Kan Cin Zarafin Bil-Adama A Kasar DR Congo
Jul 27, 2017 14:23Kwamitin Kolin Kare Hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya nada wasu kwararru uku da zasu gudanar da bincike kan rikici da tashe-tashen hankulan da suka faru a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
-
Sarkin Moroko Ya Aike Da Sakon Wasika Zuwa MDD Dangane Da Zaluncin H.K.Isra'ila Kan Palasdinawa
Jul 27, 2017 12:12Sarkin kasar Moroko ya yi tofin Allah tsine kan bakar siyasar zaluncin gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu da Masallacin Qudus mai alfarma.
-
Holland: Kotu Ta Yi Umarni Da A Gina Ma Musulmi Makaranta
Jul 27, 2017 07:51Kotun koli a kasar Holland ta bayar da umarni da a gina ma musulmi makarantar sakandare a cikin birnin Amstardam fadar mulkin kasar.
-
Faransa: Sabbin Takunkumin Amurka A Kan Iran, Rasha Da Koriya Ta Arewa Sun Saba Wa Doka
Jul 27, 2017 00:57Kasar Faransa ta sanar da cewa sabbin takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran, Rasha da Koriya ta Arewa sun yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.
-
EU Ta Damu Kan Kakabawa Rasha Takunkumi
Jul 26, 2017 11:21Kungiyar tarayya turai ta nuna damuwa akan sabbin takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Rasha.
-
Rasha Ta Mayar Da Martani Dangane Da Takunkumin Amurka
Jul 26, 2017 07:34Gwamnatin kasar Rasha ta mayar da martani dangane da sabbin rakunkuman da Amurka ke shirin kakaba mata, bayan da majalisar wakilan kasar Amurka ta amince da daftarin kudirin takunkuman a jiya.
-
An Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Wani Masallaci A Faransa
Jul 26, 2017 07:33Bangaren da ke sa ido kan kyamar musulmi a cikin kasashen nahiyar turai da ke karkashin kulawar cibiyar Azhar ya yi Allawadai da kan keta alfarmar wani masallaci na musulmi a gabashin kasar Faransa.