Rasha Ta Mayar Da Martani Dangane Da Takunkumin Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22602-rasha_ta_mayar_da_martani_dangane_da_takunkumin_amurka
Gwamnatin kasar Rasha ta mayar da martani dangane da sabbin rakunkuman da Amurka ke shirin kakaba mata, bayan da majalisar wakilan kasar Amurka ta amince da daftarin kudirin takunkuman a jiya.
(last modified 2018-08-22T07:00:27+00:00 )
Jul 26, 2017 07:34 UTC
  • Rasha Ta Mayar Da Martani Dangane Da Takunkumin Amurka

Gwamnatin kasar Rasha ta mayar da martani dangane da sabbin rakunkuman da Amurka ke shirin kakaba mata, bayan da majalisar wakilan kasar Amurka ta amince da daftarin kudirin takunkuman a jiya.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Riyabkov ya bayyana cewa, wanann mataki na Amurka zai yi tasiri wajen raunana alaka tsakanin Amurka da Rasha, kuma wadanda suka gabatar da wannan daftarin kusiri su kwana da sanin cewa ba za su iya tunzura Rasha ta yi abin da ya saba ma maslahar al'ummarta ba.

Daftarin kudirin takunkumin dai na da nufin kakaba takunkumai a kan Rasha ne bisa zarginta da yin kutse a zaben da aka gudanar a kasar Amurka, zargin da Rasha ta musunta. 

Ita  a nata bangaren kungiyar tarayyar turai tayi Allah wadai da wanann mataki na neman kakaba takunkumi a kan Rasha da Amurka ke shirin yi.