Majalisar Dattijan Amurka Ta Amince Da Kakaba Takunkumi A Kan Rasha
Majalisar dattijan kasar Amurka ta amince da kakaba sabbin takunkumai a kan Rasha, bisa zargin cewa Rasha ta yi kutse a cikin harkokin zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Amurka a cikin shekarar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoto daga birnin Washington cewa, a zaman da majalisar dattijan kasar Amurka ta gudanar a jiya Alhamis, ta amince da daftarin kudirin kakaba sabbin takunkumai a kan Rasha, a matsayin wani mataki na mayar da martani bisa tuhumar Rasha da yin kutse a harkar zaben kasar. Takunkuman dai sun hada har da kasashen Iran da Koriya ta arewa. An mika batun ga Donald Trump, inda yake da hakkin amincewa ko kuma yin watsi da shi.
Shugaban marassa rinjaye a majlaisar dokokin kasar ta Amurka Chuck Schumer, ya bayyana cewa amincewa da wannan daftarin kudiri a matsayin wata babbar nasara ga tsarin dimukradiyya a kasar Amurka.
A nasa bangaren shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, wannan mataki ba zai wuce ba tare da mayar da martani daga kasar Rasha ba.