EU Ta Damu Kan Kakabawa Rasha Takunkumi
(last modified Wed, 26 Jul 2017 15:51:36 GMT )
Jul 26, 2017 15:51 UTC
  • EU Ta Damu Kan Kakabawa Rasha Takunkumi

Kungiyar tarayya turai ta nuna damuwa akan sabbin takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Rasha.

A sanarwar da ta fitar yau Laraba, kungiyar ta EU ta ce tana mai matukar damuwa akan amuncewar da majalisar dokokin Amurka ta yi na kakabawa Rasha sabbin takunkumi.

kungiyar ta ce a shirye ta ke domin maida martani da zarar hakan zai kasance barazana ga kasashe mambobinta, muddun dai 'yan majalisar Amurka basu yi la'akari da fargabar kungiyar ba,

Dama a watan Mayu da ya gabata shugaban kungiyar ta EU Jean-Claude Juncker ya yi hannunka mai sanda ga majalisar dokoin ta Amurka kan kakabawa Rasha takunkumi ba tare da la'akari da cikas din da hakan zai haifar ga wasu kamfanonin kasashen na turai musamen wadanda ke aiki akan bututan iskar gas.

A jiya Talata ce majalisar dokokin Amurkar ta amunce da gagarimin rinjaye da kudirin gwamnatin kasar na kakabawa kasashen da suka hada da Rashar da Iran da kuma Koriya ta Arewa sabbin takunkumi, ko da yake nan gaba za'a mika kudirin ga majalisar datijan Amurkar don neman amuncewarta.