-
Mogherini: Ta Hanyar Tattaunawa Ne Kawai Za A Iya Warware Matsalolin Libya
Jul 17, 2017 13:02Babbar jami'a mai kula da harkokin siyasar wajen tarayyar turai Federica Mogherini ta bayyana cewa, ta hanyar tattaunawa tsakanin al'ummar kasar Libya ne kawai za a iya warware matsalolin da suka addabi kasar.
-
Dan Majalisar Tarayyar Turai Ya Bayyana Trump A Matsayin Maras Gogewar Siyasa
Jul 15, 2017 07:46Dan majalisar kungiyar tarayyar turai Jaromír Kohlíček ya yi kakkausar suka kan salon siyasar gwamnatin Trump, tare da bayyana shi a matsayin mutum dan kasuwa maras masaniya da rashin gogewa a fagen siyasa.
-
Bayanin Kungiyar Tarayyar Turai Kan Cikan Shekaru Da Cimma Yarjejeniyar Nukiliya Da Iran
Jul 15, 2017 01:55Babbar jami'a mai kula da harkokin siyasar waje a kungiyar tarayyar Turai ta bayyana cewa: Cimma yarjejeniya kan shirin makamashin nukiliyar Iran wata gagarumar nasara ce a fagen siyasa da tsaron yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.
-
Rasha Ta Bukaci Warware Dambaruwar Siyasar Kasar Venezuala Ta Hanyar Lumana
Jul 15, 2017 01:54Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bukaci gwamnatin Venezuala da 'yan adawar kasar da su dauki matakin dare kan kujerar tattaunawa domin kawo karshen dambaruwar siyasar kasar ta hanyar lumana.
-
WHO : Akwai Barazanar Annobar Kwalera Ta Yadu A Hajjin Bana
Jul 14, 2017 10:51Hukumar lafiya ta duniya ta ce annobar cutar amai da gudawa a kasar Yemen na iya yaduwa a yayin aikin hajjin bana a birnin Makka na kasar Saudiyya.
-
Amurka : Ba Mu Da Hujja Akan Mutuwar Jagoran IS
Jul 14, 2017 10:31Amurka ta sanar da cewa kawo yanzu ba tada wata cikakiyar hujja akan cewa an hallaka jagoran kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko kuma Da'esh cewa da Abou Bakr al-Baghdadi.
-
Adadin Musulmi Masu Zuwa Amurka Ya Ragu
Jul 14, 2017 06:12Sakamakon wani bincike ya nuna cewa adadin musulmi masu yin hijira zuwa Amurka ya ragu matuka a cikin watanni biyar da suka gabata.
-
An Gudanar Da Zanga Zangar Kin Jinin Trump A Birnin Paris
Jul 14, 2017 02:24A yayin da Shugaba Donal Trump na Amurka ke kai ziyara a kasar Faransa, Amurkawa mazauna birnin Paris sun gudanar da zanga-zangar kin jinin siyasar Shugaban na Amurka
-
Harin Jiragen Kawancen Amurka A Siriya Ya Kashe Fararen Hula Da Dama
Jul 14, 2017 02:23Kimanin fararen 10 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hari da jiragen kawancen Amurka suka kai birnin Rakka na Siriya
-
Majalisar D.D Ta Bukaci Gano Masu Hannu A Tashe-Tashen Hankulan Kasar DR Congo
Jul 13, 2017 15:01Shugaban ofishin kwamitin kolin kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya bukaci daukan matakin zakulo mutanen da suke da hannu a cin zarafin bil-Adama a yankunan da suke tsakiyar kasar.