Rasha Ta Bukaci Warware Dambaruwar Siyasar Kasar Venezuala Ta Hanyar Lumana
(last modified Sat, 15 Jul 2017 06:24:20 GMT )
Jul 15, 2017 06:24 UTC
  • Rasha Ta Bukaci Warware Dambaruwar Siyasar Kasar Venezuala Ta Hanyar Lumana

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bukaci gwamnatin Venezuala da 'yan adawar kasar da su dauki matakin dare kan kujerar tattaunawa domin kawo karshen dambaruwar siyasar kasar ta hanyar lumana.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova a jiya Juma'a ta sanar da cewa: Matakin gudanar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Venezuala da 'yan adawar kasar ne kawai zai magance dambaruwar siyasar da ta kunno kai a kasar tare da kawo karshen duk wata tarzoma da ke ci gaba da lashe rayukan mutane.

Har ila yau Maria Zakharova ta bayyana cewa: Rasha ba zata amince da duk wani tsoma bakin kasashen waje da na wasu kungiyoyi a harkokin da suka shafi cikin gidan kasar Venezuala ba, domin babu abin da hakan zai haifar banda karin ruruta wutan rikici da tarzoma a kasar.

A cikin watannin baya-bayan nan gwamnatin Amurka tana ci gaba da ingiza 'yan adawar Venezuala da nufin ganin bayan gwamnatin 'yan gurguzun kasar karkashin shugabancin Nicolas Maduro.