Amurka : Ba Mu Da Hujja Akan Mutuwar Jagoran IS
Amurka ta sanar da cewa kawo yanzu ba tada wata cikakiyar hujja akan cewa an hallaka jagoran kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko kuma Da'esh cewa da Abou Bakr al-Baghdadi.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin ministan tsaron kasar ta Amurka, Jim Mattis a yau Juma'a, bayan rahoton hallaka jagoran na IS da hukumar kare hakkin bil adama ta Syria cewa da OSDH ta fitar.
Mista Matis ya ce idan muna da masaniya a kai, zan sanar da ku, aman a yanzu ba zan iya tabbatarwa ba, ko kuma gaskatawa ba, aman a yanzu muna iya cewa yana raye don ban zan iya tabbatar da sabanin hakan ba, kuma zamu ci gaba da bibiyarsa har zuwa karshensa.
A ranar Talata data gabata ce hukumar OSDH dake da cibiya a biritaniya ta sanar da cewa an hallaka jagoran kungiyar ta IS cewa da Abou Bakr al-Baghdadi, a washe garin da kasar Iraki ta sanar da 'yanto tsohon birnin Mosul daga hannun 'yan ta'addan na Da'esh.
Hukumar ta OSDH dai ta ce wasu kusoshin kungiyar ne a yankin Deir Ezzor suka tabbatar mata da hallakar jagoran na IS, saidai ba tare bayyana lokaci, wuri ko sanadin mutuwar tasa ba.