WHO : Akwai Barazanar Annobar Kwalera Ta Yadu A Hajjin Bana
Hukumar lafiya ta duniya ta ce annobar cutar amai da gudawa a kasar Yemen na iya yaduwa a yayin aikin hajjin bana a birnin Makka na kasar Saudiyya.
Kawo yanzu dai dubban mutane ne suka mutu sanadin cutar ta kwalera a kasar ta Yemen dake fama da rikici.
A ko wacce shekara dai milyoyin musulmi ne daga ko wacce kusurwa ta duniya ke taruwa domin gudanar da aikin hajji wanda ke daya daga cikin shika-shikan musulinci.
Wanda kuma irin wannan haduwar ce a cewar hukumar ta WHO ko kuma OMS cututuka irinsu shawara, Zika, sankarau da kuma amai da gudawa ke ssamun saurin yaduwa.
Saudiyya dai ta jima bata fuskanci annobar kwalera ba saboda matakai da hukumomin lafiya na kasar ke dauka na tantance mahajjata, to saidai yadda cutar ta yi kamari a makofcciyarta Yemen inda kawo yanzu alkalumma ke cewa sama da mutane 332,000 suka kamu da cutar komi kan iya faruwa.