-
Koriya Ta Arewa Ta Sha Alwashin Mayar Wa Amurka Da Martani Idan Ta Kawo Mata Hari
Apr 15, 2017 06:24A ci gaba da rikicin da ke kokarin kunno kai tsakanin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa, kasar Korea ta Arewan ta sanar da cewa a shirye take ta mayar da martani ga duk wani harin da Amurka za ta iya kawo mata koda kuwa da makaman nukiliya ne .
-
Adadin Mutanen Da Suka Mutu Sakamakon Amfani Da Mafi Girman Bam Din Amurka A Afghanistan Ya Kai 94
Apr 15, 2017 06:24Adadin mutanen da suka mutu sakamakon amfani da wani makeken bam mafi girma da ba na nukiliya da Amurka ta yi a kasar Afghanistan sun kai mutane 94 duk kuwa da yiyuwar ci gaba da karuwar adadin saboda gagarumin karfin da bam din yake da shi.
-
Rasha Ta Fara Atisayin Soja A Yammacin Kasar
Apr 15, 2017 01:52Dakarun tsaron Rasha sun fara atisayin Soja cikin manyan tankokin yaki a yammacin kasar
-
Rikicin Kasar Ukreine Ya Lashe Rayukan Sojoji Sama 2600
Apr 15, 2017 01:51Ma'aikatar tsaron Kasar Ukreine ta sanar da mutuwar Sojojin kasar dubu biyu da 652 sanadiyar farkewar rikicin gabashin kasar
-
Ministocin Harkokin Wajen Rasha, Iran, Syria, Sun Gudanar Da Zama A Moscow
Apr 14, 2017 10:52Ministocin harkokin wajen kasashen rasha, Iran da kuma Syria, sun gudanar da wani zama na musamman a yau a birnin Moscow, domin tattauna muhimman lamurra da suka shafi halin da ake ciki a Syria, da kuma daukar matakai na hadin gwiwa a tsakaninsu domin tunkarar lamarin.
-
An Zartar Da Hukuncin Kisa A Kan Jagoran Kungiyar Jihad Islami A Bangaladesh
Apr 14, 2017 10:49An zartar da hukuncin kisa a kan jagoran kungiyar Jihad Islami a kasar Bangaladesh bisa zargin bude wa tsohon jakadan Birtaniya a kasar wuta.
-
Amurka Ta Jefa Wani Makeken Bam Mafi Girma Wanda Ba Na Nukiliya Ba A Afghanistan
Apr 14, 2017 09:08Ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta sanar da cewa ta jefa wani makeken bam da ba na nukiliya kan wani kogo da ta ce 'yan kungiyar ta'addancin nan na ISIS suke buya a ciki a kasar Afghanistan.
-
Ci Gaba Da Zanga-Zangar Nuna Kiyayya Ga Gwamnatin Venezuala
Apr 13, 2017 06:43Majiyar tsaron Venezuala ta sanar da cewa: Zanga-zangar nuna kiyayya ga gwamnatin kasar ta fara kamari a yankunan da suke kewaye da birnin Caracas fadar mulkin kasar.
-
Syria / Makamai Masu Guba : Rasha Ta Hau Kujerar Na Ki
Apr 13, 2017 01:24Rasha ta ki amincewa da wani kuduri da kasashen yamma suka gabatar, kan zargin kai hari da makamai masu guba a Lardin Idlib dake arewa maso yammacin Syria.
-
Putin: Amurka Na Shirin Yin Amfani Da Makamai Masu Guba A Syria
Apr 12, 2017 01:52Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayyana cewa, Rasha ta samu wasu bayanan sirri da ke tabbatar da cewa Amurka na shirin yin amfani da sanadarai masu guba a kusa da birnin Damascus, inda za ta dora alhakin hakan a kan gwamnatin Syria, domin samun hujjar kaddamar da wasu hare-hare a kan kasar.