Apr 15, 2017 06:22 UTC
  • Rasha Ta Fara Atisayin Soja A Yammacin Kasar

Dakarun tsaron Rasha sun fara atisayin Soja cikin manyan tankokin yaki a yammacin kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya nakalto Janar Andrei Kartapoulouf babban kwamandan Sojojin Rasha na yammacin kasar na cewa manufar wannan Atisayi na tankokin yakin kasar  gyra zama da kuma shirin ko ta kwana ga Sojojin kasar bayan ficewar lokacin sanhi.

Masana harakokin tsaron na ganin cewa kasar Rashan ta atisayi ne domin kalubalantar duk wata barazanar kasashen Yamma musaman Amurka a kan iyakokin yammacin kasar.

Shekaru da dama da kasar Amurkan ke amfani da kungiyar tsaro ta Nato wajen fadada Dakarunta a gabashin kasashen Turai dake iyaka da yammacin kasar Rasha, a cikin watanin da suka gabata, magabatan Washinton sun jibke wasu karin Tankokin yaki na zamani da kuma Sojoji gami da wasu jiragen yaki a yankin.

Magabatan Mascow sun sha nanata cewa ci gaba da kusantar Dakarun Nato da kan iyakar kasar zai aifar da mumunan sakamako, alaka tsakanin kasashen Rasha da Amurka ta tabarbare ne a shekarar 2014, bayan da Kungiyar Nato musaman ma kasar Amurka ta kara fadada Dakarunta a kan iyakokin kasar Rasha, da kuma ballewar Tsibirin Gremiya daga kasar Ukrene, sai kuma rikicin kasar Siriya ya kara dakula al'amuran.

Tags