Rikicin Kasar Ukreine Ya Lashe Rayukan Sojoji Sama 2600
Ma'aikatar tsaron Kasar Ukreine ta sanar da mutuwar Sojojin kasar dubu biyu da 652 sanadiyar farkewar rikicin gabashin kasar
Cikin wata sanarwa da ta fiyar a jiya Juma'a bayan da kasar ta cika shekaru uku cikin rikcin da ya barke a gabashin kasar, Ma'aikatar tsaron kasar Ukrene ta sanar daga lokacin fara rikicin gabashin kasar zuwa yanzu Sojoji dubu biyu da 652 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu kimanin dubu 9 da 578 suka jikkata.
Ma'aikatar ta ce duk da irin yarjejjeniyar tsagaita wuta da aka kula tsakanin Gwamnati da 'yan tawayen gabashin kasar, a shekarar bana, akalla fararen hula 21 da kuma Sojojin Ukrene 69 suka rasu.saidai sanarwa ba ta bayyana adadin Mutanen da suka rasa rayukansu a bangaren 'yan tawaye.
Rikicin yankunan gabashin kasar ta Ukrene ya fara ne a ranar 14 ga watan Avrilun shekarar 2014 kuma ya zuwa yanzu alkaluma sun bayyana cewa kimanin Mutane dubu 10 ne suka hallaka a yayin da ya jikkata wasu dubu 21 na daban.