Nov 27, 2018 06:42 UTC
  • Kasashen Jamus Da Faransa Za Su Shiga Tsakanin Rasha Da Ukraine

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Hayko Maas ne ya ba da shawarar cewa kasarsa tare da Faransa za su shiga tsakanin Rasha da Ukraine da suke rikici

Ganawa za ta gudana a tsakanin ministocin harkokin waje na kasashen Jamus, Faransda, Rasha da Ukraine,wacce an riga an shirya ta ne gabanin rikicin da ya kunno kai a tsakanin kasashen biyu.

A daren ranar Lahadi ne kungiyar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa ta tsayar da wasu jiragen ruwa guda uku na kasar Ukraine  wanda ya kai ga bude wuta. Uku daga cikin matuka jiragen na Ukraine sun jikkata.

Masu bin diddigin abin da yake faruwa suna ganin cewa jan dagar da jiragen ruwan kasashen Rasha da Ukraine su ka yi, bude wani sabon babin rikici ne a tsakanin kasashen biyu.

 

Tags