-
Sudan Ta Kudu Ta Musanta Zargin MDD Ga Sojojinta Na Yin Fyade Da Sauransu
Aug 05, 2016 05:44Kasar Sudan ta kudu ta yi watsi da zargin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na cewa sojojinta sun yi fyade da kuma kashe fararen hula a yayin da kuma bayan rikicin kabilancin da ya faru a watan da ya gabata a birnin Juba, babban birnin kasar.
-
Saudiyya Ta Fara Kwashe Mutanen Garuruwan Kan Iyaka Da Yemen Bayan Nasarorin Dakarun Yemen
Aug 05, 2016 05:43Kasar Saudiyya ta kaddamar da wani shiri na kwace mutanen yankin Jizan na kasar da ke makwabtaka da kasar Yemen biyo bayan ci gaba da kutsawa cikin kasar Saudiyyan da sojojin kasar Yemen suke yi a matsayin mai da martani da hare-haren wuce gona da irin sojojin Saudiyyan da kawayenta a kan al'ummar kasar Yemen.
-
Wani Mahari Ya kashe Mace Guda Da raunana Wasu A London
Aug 04, 2016 01:21'Yan sanda a Landon na Biritaniya sun ce wani mutun dauke da wuka ya kashe mace guda tare da raunana wasu mutane akalla shida a tsakiyar birnin.
-
Turkiya Ta Bukaci Morocco Da Ta Rufe Dukkanin makarantun Fathullah Golen
Aug 03, 2016 13:54Gwamnatin kasar Turkiya ta bukaci gwamnatin Morocco da ta rufe dukkanin makarantun Fathullah Golen da suke cikin kasarta, bisa zarginsa da take yi da hannu a yunkurin juyin mulki.
-
An Gudanar Da Zaman Tattaunawa Tsakanin Malaman Sunna Da Shi'a
Aug 03, 2016 13:34An guadanar da zaman tattaunawa a tsakanin malaman Shi'a da na sunna a kasar Pakistan, da nufin kara kusanto da fahimtar juna da kuma karfafa hadin kai a tsakanin al'ummar musulmi.
-
Wani Jirgin Saman Kamfanin Emirates Yayi Hatsari Dauke Da Mutane 275
Aug 03, 2016 06:46Kamfanin jiragen saman Emirates na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya sanar da cewa wani jirgin saman kamfanin dauke da fasinjoji da ma'aikata 275 yayi hatsari a filin jirgin saman Dubai
-
Dariruwan Kananan Yara sun Mutu a Siriya sanadiyar Ta'addancin Saudiya
Aug 03, 2016 00:56wakilin Siriya A MDD ya ce ta'addancin Saudiya yayi sanadiyar mutuwar kananan yara da dama a Siriya
-
Yan Gudun Hijira Fiye Da 4000 Ne Suka Rasa Rayukansu A Kokarin Da Suke Yi Na Shiga Kasashen Turai
Aug 02, 2016 12:42Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa; 'Yan gudun hijira da suka fito daga sassa daban daban na kasashen nihiyar Afrika, Asiya, Gabas ta Tsakiya da sauransu fiye da 4000 suka rasa rayukansu a kan hanyarsu ta tsallakawa zuwa cikin kasashen yammacin Turai a wannan shekara.
-
Mutanen Kasar Yemen Sun Bukaci A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa Don Dawo Da Zaman Lafiya A Kasar
Aug 01, 2016 13:42Zanga zangar goyon bayan kungiyar Huthi a kasar Yemen da kuma Allawadai da hare haren kasar Saudiya da kawayenta a kan mutanen kasar
-
Paparoma: Kuskure Ne A Dinga Jingina Tashin Hankali Ga Musulunci
Aug 01, 2016 06:04Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis yayi kakkausar suka ga masu yada bakar farfaganda kan addinin Musulunci biyo bayan harin ta'addancin da 'yan ta'addan kungiyar Da'esh suke kai wa Turai inda ya ce lalle babban kuskure ne a bayyana addinin Musulunci da cewa adddini ne na tashin hankali da ta'addanci.