Aug 01, 2016 10:34 UTC
  • Paparoma: Kuskure Ne A Dinga Jingina Tashin Hankali Ga Musulunci

Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis yayi kakkausar suka ga masu yada bakar farfaganda kan addinin Musulunci biyo bayan harin ta'addancin da 'yan ta'addan kungiyar Da'esh suke kai wa Turai inda ya ce lalle babban kuskure ne a bayyana addinin Musulunci da cewa adddini ne na tashin hankali da ta'addanci.

Paparoma Francis ya bayyana hakan ne a watan ganawa da yayi da manema labarai inda yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da kisan gillan da wasu 'yan ta'adda suka yi wa wani limamin kirista a kasar Faransa a kwanakin baya inda ya ce:  Ba na jin daidai ne a bayyana addinin Musulunci a matsayin addini na tashin hankali. Lalle lamarin ba haka yake ba, ba gaskiya ba ne wannan magana.

Paparoman ya ce kowane addini yana da wasu 'yan tsiraru masu tsaurin ra'ayi, mu ma muna da su. Don haka idan har za a yi maganar tashin hankali a addinin Musulunci to wajibi ne a yi irin wannan magana dangane da addinin Kirista ma.

A kwanakin baya ne dai wasu 'yan ta'addan da kungiyar Da'esh (ISIS) ta ce 'ya'yanta ne suka kai hari wani coci inda suka yankin limamin cocin, lamarin da hatta kungiyoyin musulmi na Faransan sun yi Allah wadai da shi.

Tags