Wani Mahari Ya kashe Mace Guda Da raunana Wasu A London
https://parstoday.ir/ha/news/world-i9133-wani_mahari_ya_kashe_mace_guda_da_raunana_wasu_a_london
'Yan sanda a Landon na Biritaniya sun ce wani mutun dauke da wuka ya kashe mace guda tare da raunana wasu mutane akalla shida a tsakiyar birnin.
(last modified 2018-08-22T06:58:42+00:00 )
Aug 04, 2016 01:21 UTC
  • Wani Mahari Ya kashe Mace Guda Da raunana Wasu A London

'Yan sanda a Landon na Biritaniya sun ce wani mutun dauke da wuka ya kashe mace guda tare da raunana wasu mutane akalla shida a tsakiyar birnin.

kawo yanzu dai ba'a bayyana yanayin lafiyar wadanda suka raunana ba, amma an ce matar da ta mutu ta cika ne a inda lamarin ya auku bayan zuwan 'yan agaji.

'Yan sanda birnin dai sun ce anyi nasara cafke maharin, wanda bayannan farko farko suka nuna cewa baya rasa nasaba da harin ta'addanci ta sabon salo da kungiyar 'yan ta'addan (IS) ta bullo da shi a baya bayan nan.

Saidai wasu bayyanai na daban sun ce mutumin baya rasa tabin hankali.

Dama kafin hakan a ranar lahadin data gabata shugaban 'yan sanda na birnin London, Bernard Hogan-Howe ya yi kashedi akan yiyuwar kai hare-haren ta'addanci a kasar ta Biritaniya.