-
Jakadan Siriya A Moscow Ya Ce Kasarsa Ba Ta Taba Amfani Da Makamai Masu Guba Ba
Aug 27, 2018 03:31Yayin da yake mayar da martani kan firicin baya baya nan na kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa na cewa mahukuntan birnin Damuscus sun yi amfani da makamai masu guba kan fararen hula, a daren jiya lahadi, jakadan kasar Siriya a Moscow Riyad Hadad ya ce kasarsa ba ta taba amfani da makamai masu guba, kuma ba za ta yi ba.
-
An Cimma Sabuwar Yarjejjeniyar Tsaro Tsakanin Iran Da Siriya
Aug 27, 2018 03:30Ministocin harakokin tsaron kasashen Siriya da Iran sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejjeniyar tsaro a jiya lahadi.
-
Paparoma Francis Ya Nemi Gafara Kan Cin Zarafi A Coci
Aug 27, 2018 03:30Paparoma Francis shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya ya nemi gafara Ubangiji kan laifukan da limaman coci suka yi a kasar Ireland.
-
Rundunar 'Yan Sandan Brazil Ta Kame Masu Aikata Muggan Laifuka Kimanin 3,000 A Kasar
Aug 26, 2018 14:31Rundunar 'yan sandan Brazil ta gudanar da wani samame, inda ta kame masu aikata muggan laifuka kimanin 3,000 a sassa daban daban na kasar.
-
Kasar Italia Ta Bada Sanarwan Dakatar Da Biyan Kasonta Na Kudade Da Take Bawa Tarayyar Turai
Aug 26, 2018 07:19A ci gaba da rikici kan jirgin ruwan Dichuti dauke da bakin haure tsakanin kasar Itali da tarayyar Turai ministan harkokin wajen kasar Italiya ya bada sanarwab dakatar da kudaden da ta saba bawa tarayyar Turai.
-
An Kama Wani Dan Adawa Mai Karkata Ga kasashen Yamma A Rasha
Aug 25, 2018 14:27Kakakin wata jam'iyyar Adawa a kasar Rasha ya bada sanarwan cewa jami'an tsaron kasar sun kama shugaban jam'iyyar kuma mai tsananin adawa da gwamnatin kasar a yau.
-
Rasha Ta Yi Gargadi Dangane Da Wani Yunkurin Yin Amfani Da Makami Mai Guba A Syria
Aug 25, 2018 07:36Ma'aikatar tsaron Rasha ta bankado wasu bayanan sirri da suke tabbatar da cewa, Amurka da Birtaniya gami da Faransa suna shirin sake yin amfani da makamai masu guba a Syria, domin su tuhimi gwamnatin kasar ta Syria da yin hakan.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Kakkausar Suka Kan Halin Da 'Yan Rohingya ke Ciki
Aug 25, 2018 07:34Majalisar dinkin duniya ta yi kakkausar suka dangane da irin mawuyacin halin da musulmi 'yan kabilar Rihingya suke ciki.
-
MDD Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Kananen Yara A Yemen
Aug 25, 2018 00:55Cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya juma Mataimakin saktare janar na MDD kan al'amuran jin kai, yayin Allah wadai da sabon ta'addancin kawancen saudiya a lardin Duraihimi na kusancin Alhudaidah dake yammacin kasar, tare da cewa ta'addancin ya ci rayukan kananen yara da dama.
-
Lavrov:Kasuwanci Tsakanin Kasashen Rasha Da Turkiya Ya karu Da Kashi 40
Aug 25, 2018 00:54Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, bayan ganawarsa da takwaransa na Turkiya, a birnin Moscow ministan harakokin wajen Rasha a jiya juma'a ya ce hadahadar kasuwanci tsakanin kasahen Turkiya da Rasha ya karu da kashi 40.5 a shekarar 2017 din da ta gabata.