MDD Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Kananen Yara A Yemen
Cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya juma Mataimakin saktare janar na MDD kan al'amuran jin kai, yayin Allah wadai da sabon ta'addancin kawancen saudiya a lardin Duraihimi na kusancin Alhudaidah dake yammacin kasar, tare da cewa ta'addancin ya ci rayukan kananen yara da dama.
Mista Mark Lowcock ya ce cikin makoni biyu wannan shi ne karo na biyu da kawancen saudiyar ke kai hare-hare kan fararen hula a yemen.
A marecen alhamis din da ta gabata, jiragen yakin kawancen saudiya sun kai hari kan wata mota ta 'yan gudun hijra a yankin Ku'i dake lardin Duraihimi, tare da hallaka kananen yara 27 da mata 4.
A ranar alhamis 9 da wannan wata na Augusta da muke ciki ma jiragen kawancen saudiyar sun kai wani mumunar hari kan wata motar Bas dauke da kananen yara 'yan makaranta a lardin Dahiyan na jihar Sa'ada, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar kananen yara 55 tare da jikkata wasu 77 na daban.
A nasa bangare, cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya juma'a, Asusun kananen yara na MDD Unicef ya bukaci a dakatar da yaki da kuma hallaka yaran Yamaniyawa,inda ya tabbatar da cewa a halin da ake ciki milyoyin kananen yara na yamaniya sun rasa iyayensu da ma'aifansu gami da 'yan uwansu sanadin wannan yaki.