Aug 26, 2018 11:49 UTC
  • Kasar Italia Ta Bada Sanarwan Dakatar Da Biyan Kasonta Na Kudade Da Take Bawa Tarayyar Turai

A ci gaba da rikici kan jirgin ruwan Dichuti dauke da bakin haure tsakanin kasar Itali da tarayyar Turai ministan harkokin wajen kasar Italiya ya bada sanarwab dakatar da kudaden da ta saba bawa tarayyar Turai.

Tashar talabijin ta Rai-News ta kasar Italiya ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Antouche Murovo Milanese yana sukan kasashe membobi a kungiyar tarayyar Turai, sannan ya kara da cewa kasar Italiya ba zata sake karban karin bakin haure ba.

Banda haka ministan ya bada sanarwan dakatar da biyan tarayyar ta Turai kudaden da ta saba biya a matsayin kason da ta saba biya don tafiyar da kungiyar. Amma ya kare maganar da cewa kofa a bude take a tattauna don fahintar juna a kan matsalar bakin haure a tsakanin kasashen. 

Tun ranar litinin da ta gabata ce jirgin ruwa mai suna Dichuti dauke da bakin haure 150 take tsaye kuda da tashar jiragen rauwa na Cataloniya na kasar Italia, amma ta kasa samun izinin saukesu saboda rikicin da ke faruwa tsakanin Itakiya da tarayyar ta turai.

 

Tags