Paparoma Francis Ya Nemi Gafara Kan Cin Zarafi A Coci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32925-paparoma_francis_ya_nemi_gafara_kan_cin_zarafi_a_coci
Paparoma Francis shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya ya nemi gafara Ubangiji kan laifukan da limaman coci suka yi a kasar Ireland.
(last modified 2018-08-27T03:30:02+00:00 )
Aug 27, 2018 03:30 UTC
  • Paparoma Francis Ya Nemi Gafara Kan Cin Zarafi A Coci

Paparoma Francis shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya ya nemi gafara Ubangiji kan laifukan da limaman coci suka yi a kasar Ireland.

Yayin wani jawabi da ya gabatar a babbar cocin birnin Knock da ke a nisan kilo-mita 180 da birnin Dublin,Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya ya bayyana amincewa da gazawar jagorancin mujami’u wajen daukar matakan magance aikata laifukan cin zarafin kananan yara da wasu malaman mujami’u ke yi ta hanyar yi musu fyade.

Paparoma Francis ya nemi gafarar Ubangiji kan lafuka da kuma cin zarafin da Limaman coci suka yi a kasar ta Ireland.

An bayyana cewa daga  shekara ta 2002 ya zuwa yanzu mutane sama da dubu 14 da 500 ne suka sanar da cewa limaman cocin kasar ta Ireland sun cin zarafinsu ta hanyar neman yin lalata da su ko kuma yin lalatar da su.

Fafaroma Francis wanda ya fara ziyarar tasa tun a ranar  Asabar, ya zama jagoran Kiristocin na darikar katolika na farko cikin shekaru 39, da ya ziyarci kasar ta Ireland, tun bayan Fafaroma John Paul na biyu a shekarar 1979.