-
Guinea : Babu Wani Sauran Mai Jinyar Ebola
Apr 20, 2016 23:39Hukumomi a kasar Guinea sun sanar cewa babu sauran wani mai jinyar cutar Ebola a kasar, bayan da aka sallami mutun na karshe dake jinyar cutar.
-
Kungiyar AU Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Harin Ta'addancin Da Aka Kai Kasar Habasha
Apr 18, 2016 23:55Shugabar kungiyar tarayyar Afrika ta yi tofin Allah tsine kan harin wuce gona da iri da wasu gungun mahara daga kasar Sudan ta Kudu suka kai kasar Habasha inda suka kashe adadin mutane masu yawa tare da yin awungaba da kananan yara da mata.
-
Angola Ta Wuce Najeriya Wajen Samar Da Man Fetur
Apr 16, 2016 05:52Wasu bayanai daga kungiyar kasashen masu arzikin man fetur, na cewa Najeriya ta bada matsayin da take dashi na kasa ta farko mai samar da man fetur a nahiyar Afirka.
-
Daliban Jami'ar Birnin Abidjan Na Kasar Ivory Coast Suna Ci Gaba Da Gudanar Da Zanga-Zanga
Apr 15, 2016 00:09Daliban jami'ar birnin Abidjan cibiyar kasuwancin kasar Ivory Coast sun ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana tare da kauracewa halattar darussa domin ganin mahukuntan kasar sun saki daya daga cikin jami'an kungiyar daliban jami'ar.
-
Sama da Mutane 50 ne aka yi garkuwa da su a kasar D/Congo
Apr 14, 2016 12:41Sama da Mutane 50 ne 'yan tawaye suka yi garkuwa da su a kasar D/Congo
-
Harin Grand Bassam : Ivory Coast Na Neman Wasu Mutane A Mali
Apr 14, 2016 05:12Ma'aikatar cikin gida a kasar Ivory Coast ta ce har yanzu tana neman wasu mutane da a kasar Mali da ake zargi da hannu a harin Grand Bassam.
-
Yan Adawa Sun Goyi Bayan Kudurin Majalisar Dinkin Duniya Kan Kasar DR Congo
Apr 11, 2016 06:51Yan adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congon sun jaddada goyon bayansu ga kudurin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan kasarsu musamman kiran da ya yi kan gudanar da zaben shugaban kasa a kan lokaci.
-
An Hana 'yan Adawa gudanar da zanga-zanga a kasar Angola
Apr 10, 2016 09:39'Yan Sandar Angola sun hana 'yan adawa gudanar da zanga-zanga
-
Sabuwar Gwamnatin Tsibirin Zanzibar Ta Sanar Da Kafa Majalisar Ministocinta
Apr 10, 2016 05:27Shugaban tsibirin Zanzibar da ke cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar Tanzaniya ya sanar da sabuwar majalisar ministocin kasar da ta kunshi ministoci 15.
-
Djibouti : 'Yan Adawa Sun Kalubalanci Zaben Omar Guelleh
Apr 09, 2016 10:45'Yan adawa a Djibouti sun kalubanci zaben shugaban kasar da Ismail Omar Guelleh ya lashe da gagarimin rinjaye.