Guinea : Babu Wani Sauran Mai Jinyar Ebola
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4168-guinea_babu_wani_sauran_mai_jinyar_ebola
Hukumomi a kasar Guinea sun sanar cewa babu sauran wani mai jinyar cutar Ebola a kasar, bayan da aka sallami mutun na karshe dake jinyar cutar.
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 20, 2016 23:39 UTC
  • Guinea : Babu Wani Sauran Mai Jinyar Ebola

Hukumomi a kasar Guinea sun sanar cewa babu sauran wani mai jinyar cutar Ebola a kasar, bayan da aka sallami mutun na karshe dake jinyar cutar.

A cewar hukumomin kiwan lafiya na kasar an sallami mutum na karshe dake jinyar cutar a cibiyar kula da masu fama da cutar ta Ebola.

Hakan dai ya sanya za'a sake sanya ido na wasu kwanaki 42 nan gaba domin tabbatar cewa kasar ta rabu da cutar ko kuma A'a.

A karshen watan Disamba bara ne aka sanar da murkushe cutar Ebola a kasar ta Guinea, saidai kuma kuma ta sake bulla a tsakiyar watan Maris.

An dai gano sabbin kamuwa da cutar ne a kauyen Koropara dake kudancin kasar a iyaka da kasar Laberia, bayan mutuwar wata mata data kamu da cutar.

Tun dai bayan bullar ta cikin watan Disamba na shekara a yammacin Afirka, cutar ebola ta hadassa mutuwar mutane sama da 11'300 cikin 28'000 da suka kamu da ita, galibin su kuma a kasashen da suka hada da Guinea Laberia, da Saliyo.