Angola Ta Wuce Najeriya Wajen Samar Da Man Fetur
Wasu bayanai daga kungiyar kasashen masu arzikin man fetur, na cewa Najeriya ta bada matsayin da take dashi na kasa ta farko mai samar da man fetur a nahiyar Afirka.
Bayyanan sun nuna cewa yanzu dai kasar Angola ta shige gaban Najeriya wajen samar da man fetur a Nahiyar.
Adadin man fetur din da Najeriya ke samarwa a rana daya a cewar bayanan kungiyar ta OPEP ya rage da ganga 67,000 a watan daya gabata.
Ana dai danganta wannan koma baya da Najeriya tayi wajen samar da man, da matsallin da suka hada da fasa bututan man, fasa kwabri da satar man a yankin niger delta.
Bayanin ya ci gaba da cewa an samu ci gaba wajen samar da man fetur din a kasashen da suka hada da Iran, Irak da Angola, yayin da aka fuskanci koma baya a kasashen Libya da Najeriya.