Harin Grand Bassam : Ivory Coast Na Neman Wasu Mutane A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3865-harin_grand_bassam_ivory_coast_na_neman_wasu_mutane_a_mali
Ma'aikatar cikin gida a kasar Ivory Coast ta ce har yanzu tana neman wasu mutane da a kasar Mali da ake zargi da hannu a harin Grand Bassam.
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 14, 2016 05:12 UTC
  • Harin Grand Bassam : Ivory Coast Na Neman Wasu Mutane A Mali

Ma'aikatar cikin gida a kasar Ivory Coast ta ce har yanzu tana neman wasu mutane da a kasar Mali da ake zargi da hannu a harin Grand Bassam.

Ministan cikin gida na kasar Hamed Bakayoko wanda ya ziyarci wurin shakatarwar na Grand Bassam ya ce ye zuwa yanzu sun kame mutane 83 da ake zargi da kai harin na ranar 13 ga watan Maris da yayi sanadin mutuwar mutane 19.

kafin hakan dama an cafke wasu 'yan kasar ta Mali biyu wadadan ake zargi da hannu wajen kai harin na Grand Bassam.