-
MDD Ta Bada Taimakon Dala Miliyan 10 Ga wadanda Guguwar Irma Ta Rutsa Da Su.
Sep 18, 2017 07:47Jami'i mai kula da ayyukan agaji da ceto na Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock Ya ce za a yi amfani da kudaden ne domin sayan kayan abinci da kiwon lafiya.
-
Koriya Ta Arewa Na Daf Da Mallakar Makamin Nukiliya
Sep 16, 2017 01:14Shugaba Kim Jong-Un, na Koriya ta Arewa ya ce kasarsa na daf da mallakar makamin nukiliya, wannan kuwa duk da jerin takunkuman da kasashen duniya ke kakaba ma kasar ta sa.
-
A Cikin Shirin Korar Baki: Amurka Zata Dakatar Da Bada Wasu Nau'in Visa A Wasu Kasashe
Sep 14, 2017 00:59Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta dakatar da bada wasu nau'in Visa ga wasu kasashe daga jiya Laraba a cikin shirin gwamnatin Donal Trump na korar baki daga kasar.
-
MDD Ta Kakabawa Koriya Ta Arewa Sabbin Takunkumai
Sep 12, 2017 01:20Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da kudirin Amurka na tsananta wasu jerin sabbin takunkumai kan Koriya Ta Arewa bisa gwajin makamin nukiliyarta na baya baya nan.
-
Dan Majalisar Amurka John McCain Ya yi Wa KoreaTa Arewa Barazanar Shafe Ta Daga Doron Kasa
Sep 11, 2017 02:53John McCain wanda shi ne shugaban kwamitin Tsaro a majalisar dokokin Amurkan ya ce; Matukar Korea ta kai wa Amurka ko kawayenta hari,to za a shafe ta daga doron kasa.
-
Amurka Ta Bukaci A Kada Kuri'ar Kakabawa Koriya Ta Arewa Sabbin Takunkumi
Sep 09, 2017 01:14Amurka, a hukumance, ta bukaci a gudanar da zaman Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya don kada kuri'a kan daftarin kudurin da ta gabatar don kakabawa Koriya ta Arewa sabbin takunkumi saboda gwajin makaman nukiliya da ta yi kwanakin baya.
-
Tunusiya Ta Karyata Labarin Cewa Akwai Sansanin Sojin Amurka A Cikin Kasarta
Sep 08, 2017 02:09Ministan tsaron Tunusiya ya karyata labarin cewa: Kasar Amurka ta kafa sansanin sojinta a cikin kasar Tunusiya.
-
Jiragen Yakin Kawancen Amurka Sun Kashe Mutane 14 A Garin Rakka
Sep 03, 2017 14:25Masu rajin kare hakin bil-adama na kasar Siriya sun bayyana cewa harin da jiragen yakin kawancen Amurka suka kai garin Rakka ya kashe fararen hula 14.
-
Rasha Ta Zargi Amurka Da Keta Tsarin Diflomasiyya
Sep 03, 2017 02:02Kasar Rasha ta zargi Amurka da keta kariya diflomasiyya ta hanyar kai samame a ginin tawagar kasuwancinta a birnin Washington.
-
Rasha Ta Ja Kunnen Amurka Dangane Da Siyasar Kiyayya Da Take Nuna Mata
Sep 02, 2017 06:24Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewar kasar Rasha za ta mayar da kakkausan martani ga matakan nuna kiyayya da Amurka take dauka a kan kasarsa a daidai lokacin da kai ruwa ranar da kasashe biyu suke yi ke ci gaba da kamari.