Jiragen Yakin Kawancen Amurka Sun Kashe Mutane 14 A Garin Rakka
Masu rajin kare hakin bil-adama na kasar Siriya sun bayyana cewa harin da jiragen yakin kawancen Amurka suka kai garin Rakka ya kashe fararen hula 14.
Kamfanin dillancin labaran Sana na kasar Siriya ya nakalto cibiyar kare hakin bil-adama ta kasar Siriya na cewa a jiya Assabar jiragen yakin kawancen Amurka sun yi ruwan bama-bamai a yankin Dawari-Na'im dake garin Rakka, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar fararen hula 14 tare da jikkatar wasu da dama na daban.
A makon da ya gabata ma jiragen yakin kawancen Amurkan sun yi ruwan bama-bamai a wuraren dakarun kurdawan Siriya na garin Rakka, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 15.
Tun daga watan Augustan 2014 ne kasar Amurka tare da kawayanta ba tare da izinin magabatan kasar Siriya ba da kuma MDD suka fara kai farmaki kan al'ummar kasar Siriya bisa riyar yaki da kungiyar ISIS,
A yayin da rahotanni ke cewa magabatan Amurka da kawayenta na kasashen yamma da Larabawa su ne suka kirkiro kungiyar ta IS tare da taimakawa musu da kudi gami da makamai.