Tunusiya Ta Karyata Labarin Cewa Akwai Sansanin Sojin Amurka A Cikin Kasarta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23827-tunusiya_ta_karyata_labarin_cewa_akwai_sansanin_sojin_amurka_a_cikin_kasarta
Ministan tsaron Tunusiya ya karyata labarin cewa: Kasar Amurka ta kafa sansanin sojinta a cikin kasar Tunusiya.
(last modified 2018-08-22T11:30:39+00:00 )
Sep 08, 2017 06:39 UTC
  • Tunusiya Ta Karyata Labarin Cewa Akwai Sansanin Sojin Amurka A Cikin Kasarta

Ministan tsaron Tunusiya ya karyata labarin cewa: Kasar Amurka ta kafa sansanin sojinta a cikin kasar Tunusiya.

Farhat Al-Harshani ministan tsaron kasar Tunusiya a jiya Alhamis ya fito ya bayyana cewa: Tunusiya ta kulla yarjejeniyar tsaro da wasu kasashe irin Faransa, Amurka, Belgium da Aljeriya amma hakan baya nufin cewa; Gwamnatin Tunusiya ta bai wa wata kasa damar kafa sansanin sojinta a cikin kasar Tunusiya.

Har ila yau ministan tsaro kasar ta Tunusiya ya bayyana cewa: Duk da barazanar ayyukan ta'addanci da kasarsa take fuskanta musamman sakamakon matsalar rikicin kasar Libiya da tashe-tashen hankulan da suke faruwa a yankunan arewacin Afrika, kasar Tunusiya tana da karfin kalubalantar wadannan hatsari da barazana musamman ta hanyar gudanar da taimakekkeniya da kasashen da ta kulla yarjejeniyar tsaro da su, amma hakan baya nufin cewa: Wata kasa daga cikin kasashen ta kafa sansanin sojanta a cikin kasar Tunusiya.

A kwanakin baya-bayan nan ne wasu kafofin watsa labarai suka watsa rahoton cewa: Kasar Amurka tana da sansanin soji a yankin Sayyidi Ahmed da ke shiyar arewacin kasar Tunusiya.