Rasha Ta Zargi Amurka Da Keta Tsarin Diflomasiyya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23723-rasha_ta_zargi_amurka_da_keta_tsarin_diflomasiyya
Kasar Rasha ta zargi Amurka da keta kariya diflomasiyya ta hanyar kai samame a ginin tawagar kasuwancinta a birnin Washington.
(last modified 2018-08-22T07:00:38+00:00 )
Sep 03, 2017 02:02 UTC
  • Rasha Ta Zargi Amurka Da Keta Tsarin Diflomasiyya

Kasar Rasha ta zargi Amurka da keta kariya diflomasiyya ta hanyar kai samame a ginin tawagar kasuwancinta a birnin Washington.

Rasha ta bayyana hakan ne a yayin da ta kirayi babban jami'in diflomasiyyan Amurka da ke birnin Moscow a jiya Asabar.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce an kirayi Anthony Godfrey domin mika masa wasika jin takaicin samamen da aka kai a ginin na ta.

A ranar Juma'a da ta gabata ce ma'aikatar diflomasiyyan ta Rasha ta sanar da cewa jami'an binciken FBI na tunanin binciken karamin ofishin jakadancinta na San Francisco wanda mahukuntan Washigton suka bada umurnin rufewa tare da ofishin kasuwancinta na Washington da New York.

Amurka dai ta ce ta dau matakin ne don maida martani ga Rasha saboda rage jami'an diflomasiyyanta dake birnin Moscow na Rashar.